Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa


Mutane akan layin zaben kananan hukumomi a jihar Nasarawa

A zaben kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa da aka yi a karshen mako, jam’iyyar APC ce ta lashe kujerun shugabannin 13 tare da duka kansilolinsu 147 yayinda jam’iyyar PDP ta kauracewa zaben bisan zargin cewa ba za’a yi mata adalci ba.

Jam’iyyar APC ta lashe zaben shugabannin kananan hukumomi 13 tare da duk kansilolin da aka yi a karshen makon jiya.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Henry Omakpu wanda ya bayyana sakamakon zaben ya ce jama’iyyar ta kuma lashe kujerun kansiloli 147 dake jihar. A cewarsa bisa ikon da dokar zabe ta jihar ta bashi ya ce ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya daya tilo da ta yi nasara a duk zabukan kananan hukumomin jihar.

Shugaban hukumar zaben ya ce duk abubuwan da suke nema da suka jibanci ayyukansu gwamnatin jihar ta basu kuma sun yi aikinsu yadda ya kamata. A cewarsa jam’iyyar PDP ta nuna masu bata yi cikakken shiri ba. Amma su sun yi kokarinsu sun kuma yi adalci.

Jam’iyyu 21 ne suka shiga zaben baicin ita PDP da ta kaurace bisa zargin cewa ba za’a yi mata adalci ba. Shugaban jam’iyyar a jihar Francis Orogbu ya ce wadanda aka nada jami’an hukumar zaben duk ‘yan jam’iyyar APC ne. Na biyu a lokacin da ake gab da fara zaben aka soma canza dokin zabe inda har aka hana sanarda sakamakon zabe a gunduma gunduma wai sai an kai hedkwata, saboda haka suka umurci jama’arsu kada ma su bata wa kansu lokaci su gujewa zaben, a cewarsa.

Amma sakataren jam’iyyar APC na jihar Alhaji Aliyu Bello ya ce an samu nasara ne saboda basu da hamayya a ciki da wajen jam’iyyar. Ya ce a jihar kowa ya san tun shekarar 2011 da suka fito daga CPC suka koma APC basu da wata matsala.

Gwamnan jihar Umar Al-Makura ya ce karo na biyu ke nan da gwamnatinsa ta gudanar da zaben kananan hukumomi saboda haka burinsu na tabbatar da kafuwar Dimokradiya a jihar ya cika.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG