Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar BJP Mai Hamayya A India Ta Sami Gagarumin Nasara A Babban Zaben Kasar.


PM India mai jiran gado Narenda Modi.
A India shugaban ‘yan hamayya Narenda Modi, yayi alkawarin zai yi aiki domin jama’ar kasar baki daya, bayanda jam’iyyarsa ta BJP ta sami gagarumar nasara a zaben kasar da aka gudanar.

Kwariya-kwariyar sakamakon zabe da aka bayyana ya nuna jam’iyyar Modi da ake kira BJP ko Bharatiya Janata, ta kada jam’iyyar CP mai mulkin kasar da gagarumar rata.

PM mai jiran gado yayi jawabi ga dumbin magoya bayansa wadanda suke cike da murna jiya jumma’a, inda ya lashi takobin gwamnatins a zata yi aiki ga dukkan ‘yan kasar.

Shugabar jam’iyyar CP mai mulkin kasar Sonia Ghandi ta amince jam’iyyarta ta sha kaye. Shugabar tareda da danta Rahul Ghandi wanda shine mataimakin shugaban jam’iyyar, wadanda suka jagoranci yakin neman zaben da aka yi , sun dauki laifin faduwarda jam’iyyar tayi.

Jam’iyyar CP ko congress party ta jagoranci India fiye da shekaru 10 da suka wuce, ta fuskanci manya manyan abun fallasa ta fuskar cin hanci da rashawa, tashin farashin kayayyaki, da kuma rashin ci gaban tattalin arzikin kasar.
XS
SM
MD
LG