Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Democrats Ta Amurka Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Virginia da Jihar New Jersey


Sabon Gwamnan Jihar Virginia Ralph Northam, dan jam'iyyar Democrats
Sabon Gwamnan Jihar Virginia Ralph Northam, dan jam'iyyar Democrats

Jam'iyyar Democrat a nan Amurka ta lashe zabukan gwamnonin jihohin Virginia da New Jersey ta kuma lashe kujerun wasu 'yan majalisu da na mataimakin gwamna da antoni janar

Jiya Talata ta kasance ranar farin ciki ga ‘yan Democrat a Amurka bayan da jam’iyar ta lashe zaben gwmanonin da aka yi a wasu jihohi.

Dan takarar Democrat, Ralph Northam ya lashe zaben jihar Virginia, wanda ya kasance zazzafa, inda ya doke abokin hamayyarsa Ed Gillespie, nasarar da ta bashi damar maye gurbin gwamna mai barin gado, Terry McAullife, wanda dan jam’iyar ta Democrat ne.

A jihar New Jersey kuwa, dan takarar jam’iyar ta Democrat, Phil Murphy ya samu galaba akan abokiyar hamayyarsa Kim Guadagno, ‘yar Republican, inda zai maye gurbin gwamna mai barin gado, Chris Christie na jam'iyyar Republican.

Phil Murphy dan jam'iyyar Democrat sabon gwamnan New Jersey tare da tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama
Phil Murphy dan jam'iyyar Democrat sabon gwamnan New Jersey tare da tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama

Dama dai ana sa ran dan takarar na Democrat shi zai lashe wannan zabe.

Har ila yau a zaben na Virginia, dan takarar Democrat Danica Roem ya samu nasara akan Robert Marshall, nasarar da ta bashi damar zama dan majalisar dokokin jihar na farko da ya fito fili ya bayyana cewa ya sauya jinsinsa.

Wannan zabe da aka yi a jiya Talata, zai iya zama mahangar yadda masu kada kuri’a suke kallon kamun ludayin gwamnatin shugaba Trump, yayin da jam’iyun biyu ke ta da tsiminsu domin tunkarar zaben rabin wa’adi da za a yi a badi a duk fadin Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG