Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Dimokarat Ta Kama Hanyar Sake Lashe Wani Muhimmin Zaben Majalisa a Amurka


Dan takarar Dimokarat Conor Lamb

A wani al'amari da zai kara ma 'yan jam'iyyar Dimokarat gwiwa, tankarar Majalisar Dokokinsu na Pensylvania, ya kama hanyar doke na Republican.

Dan takarar jam’iyyar Dimokrat Conor Lamb ya yi shelar yin nasara da safiyar yau Laraba, a zaben Majalisar Wakilan Amurka na musamman na kujerar wata gundumar da ke wajen Pittsburgh a jahar Pennsylvania.

Saidai har yanzu jami’an zabe bas u fitar da sakamakon karshe na zaben na jiya Talata ba, kuma da wuya kafofin yada labarai su iya hasashen wanda zai yi nasara saboda tazarar da ke tsakanin ‘yan takarar, wato Lamb na Dimokrat da Rick Saccone na Republican, ba ta da yawa.

Zuwa daren jiya, a lokacin da ake kidaya kuru’un wadanda su ka kada daga nesa, Lamb na jam’iyyar Dimokrat na kan gaba da adadin kuru’u 500 daga cikin kuru’u sama da dubu 227 da aka kidaya.

Lamb, wani tsohon sojin ruwan Amurka dan shekaru 33 da haihuwa kuma tsohon lauya mai gabatar da kara, ya ayyana nasara a jawabinsa ga magoya baya, inda y ace da su, “We yi nasara.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG