Akwai manyan kusoshin jam'iyyar ta MODEN LUMANA a hannun hukumomin Nijar da ake zarginsu da aikata ba daidai ba kamar yin rub da ciki da dukiyoyin jama'a inji gwamnati.
Baicin wadannan yau sama da shekara guda ake tsare da wasu jigajigan jam'iyyar a gidan kaso. Akwai kuma wadanda ake tsare dasu saboda wai sun wawure dukiyar kasa. To saidai MODEN LUMANA tace bita da kulin siyasa ne.
Alhaji Lawali Salisu Bece kusa a cikin jam'iyyar yace abubuwan da ake yiwa 'ya'yansu zargi ne kuma ko 'yan kasa sun gane sharri ne kawai saboda wai an yi nazari an ga cewa idan an kama shugabanninsu na jihohi za'a hana wa jam'iyyar samun kuri'o'i lokacin zabe.
Akwai wasu ma da an dade da kamesu amma har yanzu suna tsare ba'a yi masu shari'a ba.
To amma Alhaji Kalla Hankurau kusa a kwamitin koli na jam'iyyar PNDS mai mulki yace labarin ba haka yake ba. Yace su fadi wadanda aka kama baicin wadanda suka yi kokarin juyin mulki. Sai kuma wadanda suka aikata aikin asha kuma idan ba'a yi masu shari'a ba babu wanda zai tabbatar sun aikata laifin. Ya kamata su jira shari'a tayi aikinta. Yace wadanda ma aka kama ba 'yan MODEN LUMANA ba ne.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.