Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamiyyar PDP A Jihar Kebbi Tace Zata Kalubalanci Hukumar Zabe Da Jamiyyar APC A Kotu


Niger Elections

Hukumar zaben jihar ta Kebbi ta fitar da sunayen ‘yan takarar zaben majilisun kananan hukumomi daga jamiyyu kusan 26, to amma ba na babban jamiyyar adawa ta PDP.

Hakan yasa jamiyyar ta PDP zargin hada bakin hukumar zaben da jamiyyar APC mai mulki domin hana su shiga zaben.

Umar Na Amore shine dan takarar shugabancin karamar hukumar mulki ta Argungu karkashin inuwar jamiyyar ta PDP, ga kuma korafin da yayi a hira da wakilin sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna yayi da shi.

‘’Ance mu kai takardun mu na ‘yan takara, mun kai a ranar 27, lokacin da ita shugaban hukumar zaben ya kira shugaban jamiyya cewa an kara wa’adin lokacin gudanar da zaben da sati guda bisa lokacin da suka sa na karban sunayen ‘yan takarar da za’a yi zaben da su. Bayan mun kai, an karba. Daga baya hukumar zabe ta kira shugabannin mu cewa suzo su karbi sunayen akan cewa mun wuce lokacin da aka ce a karbi takardun mu. Lokacin da aka ce an kara wa sati guda, ya kai kafin wannan lokacin ake cewa ya wuce?.

Sai dai hukumar zaben ta jihar Kebbi ta musunta wadannan zarge-zargen, kamar yadda shugabanta Aliyu Mohammed Mera ke cewa.

‘’Kasan Al’amurran mutane ko baka wa kanka adalci ba sai kayi kokari ka aza ma wani. Abinda aka ce shine za rufe a ranar 26 ga wata, baka kawo ba sai 2 ga wata na wani watan da ya shigo,lokacin ka kawo to yanzu wanene baiyi adalci ba?.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG