Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar PDP Bangare Makarfi Ta Zargi Gwamnatin APC


ABUJA: Taron PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi

Jami’an tsaro sun yi yunkurin dakatar da wani taron jam’iyyar PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi a Abuja, yayin da bangaren Makarfin ke zargin gwamnatin APC da hada baki da bangaren Sanata Ali Modu Sheriff, don wargaza jam’iyyar PDP.

Tun ranar Alhamis ne dai kotun ‘daukaka ‘kara a Fatakwal ta yanke hukunci da ya baiwa Sanata Sheriff shugabancin jam’iyyar PDP. Bangaren Makarfi dai sun shirya gunadar da wani taro jiya Litinin a Abuja, biyo bayan yunkurin jami’an tsaro na dakatar da taron hakan yasa suka dunguma zuwa gidan gwamnan jihar Ekiti dake Abuja.

A daren jiya dai jam’iyyar PDP bangaren Makarfi suka zargi gwamnatin APC da laifin yin amfani da bangaren Sanata Sheriff don wargaza jam’iyyar ta su. A cewar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, “wanda yake mulki yana son zuciyarsa” ya ci gaba da cewa amfani da ‘yan sanda ko kotu ba zai canzawa ‘yan jam’iyyar zuciyarsu ba kuma zasu gyara kansu nan bada dadewa ba.

Amma jam’iyyar APC mai mulki ta nesanta kanta daga rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP. Sakataren jam’iyyar APC na ‘kasa Alhaji Mai Mala Buni, yace tun kafin ayi zaben shugaban ‘kasa Sanata Sheriff ya bar APC, wanda a lokacin sune suka janyo shi suka bashi shugabanci. Ya ci gaba da cewa babu wani abu da ya shafi ‘yan jam’iyyar APC, kuma shugaba Buhari bai taba amfani da jami’an tsaro ba wajen hana wata jam’iyya motsi.

Sule Lamido ya nanata kudurinsu na ‘daukaka ‘kara a kotun koli domin kalubalantar hukucin kotun ‘daukaka ‘kara da ta tabbatarwa Sanata Modu Sheriff shugabancin jam’iyyar PDP.

Domin karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG