Jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta musanta zargin da ake yi mata na cewa ita ce ta ke yin makarkashiya saboda a daga zaben Najeriya har zuwa wani lokaci.
Babbar jam’iyyar Adawa a Najeriya ta fito fili ta nuna kin amincewa da maganar daga zabe, da a halin yanzu yafi komai daukar hankali a fagen siyasar Najeriya, wani abu da ya zama kamar mayarwa wadansu jam’iyyu goma sha shida martani bayan da suka hada kai suka fito da matsaya ‘daya, a wata takarda mai dauke da sa hannun su cewa a ‘dage zaben domin hukumar zabe ta samu damar bada katunan zabe na din din din tukunna kafin a cigaba da yin zaben.
Duka da wadannan kiraye kirayen dai ‘yan siyasa na cigaba da yakin neman zaben su, sannan kuma kungiyoyi masu kare dimokaradiyya na cigaba da tarurruka babu dare babu rana, tare da yin amfani da kafofin yada labarai wajen yin kira ga janyo hankalin ‘yan kasa a game batun dage zaben.
A lokacin da kakakin kwamitin kamfen na Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode, yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu akan ko jam’iyyar PDP na goyon bayan dage zaben, yace, “Shawarar daga zabe ko jinkirtashi, hurumine na hukumar zabe babu hannun shugaba Jonathan ko na ‘dan jam’iyyar PDP a wannan kira.
Saurari cikakken rahotan Madina Dauda.