Accessibility links

Hadewar da wasu 'yan tawayen gwamnoni biyar suka yi da sabuwar jam'iyyar APC ta sa tsohuwar PDP ta farfado a jihar Sokoto kuma ta tashi gadan gadan.

Shugaban tsohuwar jam'iyyar PDP kuma tsohon ministan sadarwa Alhaji Arzika Tambuwal ya yi jawabi a wani babban taron jam'iyyar na mayarda martani kan matakin gwamnan jihar na shiga kawance da sabuwar jam'iyyar APC.

Taron na tsoffin shugabannin PDP ne da a da can suka bace. Manyan kuwa sun hada da dan takarar gwamna Sanato Abdalla Wali da Abubakar Umar Gada da Garba Ila Gada da sauran manyan kusoshin jam'iyyar na farko. Dukansu sun nuna muba'ayarsu ga jam'iyyar PDP a karkashin Bamanga Tukur.

A jawabinsa wurin taron Alhaji Arzika Tambuwal yana ganin ballewar gwamna Wamako zuwa jam'iyyar APC wata dama ce ta samu na dawo da jam'iyyar PDP a hannunsu wadda ya ce dama kwace aka yi masu. Dangane da ko sun makara Alhaji Tambuwal ya ce ba kullum ya kamata mutum ya fito ba. Amma yanzu da yake akwai matsala lokaci ne na fitowa domin wadanda suka surkasu sun fita. Don haka zasu iya tara kansu su gyara jam'iyyarsu su cigaba da yakin da suke yi. Ya ce wannan shigan da Wamako da mukarrabansa suka yi ba tare dasu ba ne kuma ba zasu bisu zuwa APC ba.

Tuni dai gwamna Wamako ya amince da kawancen da gwamnoni biyar suka shiga da APC.Wani na hannun daman gwamnan kuma mataimakin sakataren sabuwar PDP Umar Modi Hiliya ya ce sun amince da kawancen domin mulkin kama karya da rashin adalci a jam'iyyar PDP. Ya ce rashin adalcin ya yi yawa shi ya sa suka nemi a gyara domin a kawo adalci cikin jam'iyyar.

Murtala Faruk Sanyinna nada rahoto.

XS
SM
MD
LG