Accessibility links

Jam'iyyar PNDS Mai Mulki a Niger ta Zabi Sabon Shugaba


Taron jam'iyyu a Niger

Bayan 'yan jam'iyyar PNDS sun gama taron kwana biyu sun zabi sabon shugaba

Jam'iyyar PNDS ta yi taronta na kasa ba shugaban kasar Yousouf Muhammed inda daga karshe ta zabi sabon shugaba.

Taron ya kammala da zaben sabbin shugabanni da zasu jagooranci jam'iyyar har na tsawon shekaru hudu. Sabon shugaban wanda shi kadai ne ya tsaya shi ne shugaban riko Malam Bazu Muhammed. An zabeshi da kuri'u 113 daga cikin wakilai 113 wadanda suka cancanci yin zabe.

Da yake jawabi sabon shugaban ya ce abubuwan da zai sa gaba su ne kyawawan halaye da tsohon shugaban jam'iyyar Yousouf Muhammed ya koya masu wadanda suka hada da adalci, gaskiya, rikon amana, rike kowa ba tare da nuna banbanci ba da guje ma duk abun da ya karya doka da son kowa.Malam Kalla Mukhtari dan jam'iyyar PNDS kuma gwamnan jihar Zinder ya ce yana murna sun rike amana kansu kuma ya hadu sun yi zabe cikin lumana. Ya ce Yousouf ya jagoranci jam'iyyar na shekara ashirin kana wanda suka zaba 'yanzu shi ma ya yiwa Yousouf mataimaki na shekara ashirin sai gashi yau ya zama shugaba.

Dangane da abun da 'yan jam'iyyar ke fatan gani daga shugabansu dan majalisar dokokin kasar kuma dan majalisar zartsawar jam'iyyar Sani Bukari ya ce sabon shugaban ya koyi tarbiya irin ta wanda ya gada. Yanzu sai a sa ido a ga abubuwan da ka biyo baya domin PNDS ta ce dan takararta a zaben 2016 Yousouf Muhammed ne.

Abdullahi Mammman Ahmadu nada rahoto.
XS
SM
MD
LG