Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jana'izar Dan-masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule


Tsohon Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule, Abuja, Nigeria, Thursday, March 17, 2011

Dubban jama'a sun halarci jana'izar Tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda ya rasu a farkon makon nan.

An yi jana’izar Ministan mai na farko a jamhuriya ta farko a Najeriya, kuma tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Dan- masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule.

Dubun dubatar ‘yan Najeriya ne suka halarci sallar jana’izar da Limamin babban Masallacin kano Parfessa Mohammed Sani Zaharudeen ya jagoranta.

Daya daga cikin daliban marigayin, Alhaji Sale Aliyun Hadeija, yace wannan gibi zata yi wuyar cikewa, saboda matsayinsa da shugabancinsa ba a arewa kadai ba, amma a fadin kasar baki daya.

Shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari ne ya jagoranci tawagar banagaren zartaswa, yayinda shugaban majalisar dattijai Senata Bukola Saraki ya jagoranci bangaren majalisa.

Gwamnoni da sarakunan gargajiya ciki da wajen kasar ne suka halarci jana’izar.

An binne Alhaji Yusuf Maitama Sule ne a makabartar da take kofar Mazugal.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG