Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Abdul Lela Usman Ibn Al-saleh Ya Halarci Bukin Kaddamar Da Gidan Radiyon Da Soji Suka Kafa a Maiduguri


Mukaddashin sakatare Janar na wasu kasashen Muslmi masu yaki da ta’addanci Laftanar Janar Abdul Lela Usman Ibn Al-saleh, ya ce kaucewa koyarwar Kur’ani da Hadisin manzon Allah (SAW) ne ke haifar da tsageranci, daga nan kuma sai a fada zuwa ta’addanci.

Mukaddashin sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da ake kaddamar da wani gidan radio mallakar sojin Najeriya, da ake kira Ofishin Lafiya Dole Radio, a garin Maiduguri.

Da yake jawabi, Abdul Lele, ya bayyana cewa ya ziyarci wannan bangare na kasar ne domin tattaunawa da abokan aikinsa sojojin Najeriya, domin ganin yadda zasu bullowa wannan matsala ta ta’addanci.

Ya ce kafa wannan gidan Radio, ya nuna irin wayewar da wannan kasa take da ita musamman ta yadda sojin kasar zasu kawo karshen ta’addanci, ya kuma kara da cewa ta’addaci na zuwa ne a sakamakon tsageranci, kuma tsageranci na zuwa ne a sakamakon kaucewa koyin addinin Islama, kamar yadda yake a Qur’ani, da kuma litattafan Sunnah.

Daga karshe Laftanar Janar Abdul, ya bayyana cewa zasu duba wasu abubuwa da kuma hanyoyin da suka dace domin bada tasu gudummuwa ta yaki da ta’addanci a arewacin Najeria .

Babban kwamandan yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Birg, Janar Usman Sani Kuka Sheka, ya bayyana cewa makasudin gina wannan gidan Radio, shine domin a wayar wa da jama’a kai, domin yaki da ta’addanci ba aikin jami’an tsaro kadai bane ya zama wajibi a nemi hadin kan jama’a da fahimtar dasu domin a tabbatar da magance wannan matsala ta ta’addanci.

Dan haka wannan gidan radio, zai rika watsa labarun duniya da kuma fadakarwa da wa’azi da jawo hanaklin jama’a da kuma nishadantarwa, za a kawo tsare tsare da jama’a zasu yi na’am dasu yadda ta haka ne za a jawo hanakalinsu domin canza al’kiblar wadanda suka kangare.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG