Accessibility links

Anga wasu motoci dauke da makamai a lokacin ziyarar Janar Muhammadu Buhari Maiduguri.

A lokacin da ake kokarin tarbon dan takarar shugabancin Najeriya, na jam’iyyar adawa a garin Maiduguri, Janar Muhammadu Buhari, sai gashi wasu matasa sunyi sa'insa da jami’an tsaro, akan wasu motoci guda biyu da suke dauke da makamai.

Wadannan matasan sun ga wannan motocin suna kokarin wucewa inda suka nemi da a bude wadannan motocin don ganin meke ciki, amma sijojin da ke a wannan wurin basu yarda da a bude don ganin abun da ke cikin motar ba, wannan dai ya kawo rashin jituwa tsakanin sojojin da wasu matasa masu kokarin kawo kwanciyar hankali a jihar.

Bayan abubuwa sunyi tsamari, sojojin dai sun harbi mutane hudu. Bayan wannan abun ya lafa ne sai ga dan takarar shuagabancin Najeriya, ya iso garin, yakuma kai ziyarar ban girma a fadar me martaba Shehun Barno. Daga bisani ya isa wajen taron gangamin neman zabe, wanda bayan isarshi ake ta harbe harben bindigogi, kuma mutane da dama sun raunata wanda wasu kuma suka mutu a sanadiyyar turereniya da akayi don nunama dantakarar kauna, daga mutanen jihar.

XS
SM
MD
LG