Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ke Jawo Tabarbarewar Tarbiyyar Yara?


Wadansu Yara A Aji
Wadansu Yara A Aji

Tarbiyyar yara na ci gaba da fuskantar barazana a Jamhuriyar Niger, abinda mahukuntan ke dorawa akan amfani da shafukan sada zumunci.

Taron mahawarar bainar jama’a na kawancen CONGAFEN na kungiyoyin kare hakkin mata don tattaunawa akan wannan sabon al’amari dake fayyace illolin da tabarbarewar tarbiyya ta haddasa da kuma irin barazanar da hakan ke yi wa zamantakewar al’umma.

Hajiya Fatima madam kako itace shugabar kawancen na CONGAFEN, ta bayyana dalilin da ya sa sukai wannan zaman tattaunawa wanda shi ne domin duba fuskar tarbiyyar yara mata da ta tabarbare, ta bayyana yadda ake kama cutar 'sida', abin da ya zama ruwan dare a yankin.

Hajiya Nafisa Agada ta bayyana cewa yawan amfani da shafukan sada zumunta na daga cikin abubuwan da ke ingiza matasa rungumar dabi’un da ke jefa su cikin hadarin kamuwa da cututuka makamanta 'sida,' ta kara da cewa har da iyaye mata da ba sa maida hankali wajen kula da ‘ya’yan su , da son abin duniya na yara kanana na ganin abinda wasu ke da shi su ma suna so su samu.

Ministar ci gaban mata da kare hakkin yara ta Nijar, Hajiya Zainabu El bak Adam ta bayyana cewa tuni gwamnatin Niger ta yi nisa wajen neman hanyoyin da za su taimaka wajen taka wa wannan matsala birki, ta kuma yi kira ga iyaye da su saka ido kan yaran su inda ta kara da cewa tarbiyya daga gida take farawa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG