Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janyewar Amurka Ya Jefa Yarjejeniyar Nukiliyar Iran Cikin Hadari


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD Antonio Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD Antonio Guterres

Rosemary DiCarlo dake aiki da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta ce janyewar da Amurka ta yi ya jefa yarjejeniyar nukiliyar Iran cikin hada lamarin da ya damu babban sakataren

Shugaba a fannin siyasa na Majalisar Dinkin Duniya, ta ce matsayar da aka cimma ta nukiliyar Iran na cikin “tsaka mai wuya” bayan da Amurka ta janye daga wannan yarjejeniya a watan da ya gabata.

A cewar Rosemary DiCarlo, mai kula da harkokin siyasa a majalisar, Sakatare Janar, ya nuna takaicinsa matuka, kan wannan koma-baya da aka samu kan matsayar ta nukiliyan Iran, wacce aka cimma a shekarar 2015 wacce kuma ake wa lakabi da Joint Comprehensive Plan of Action ko kuma “JCPOA” a takaice, tana mai cewa, kamata ya yi a tunkari matsalolin da ke tattare da matsayar ba tare da an nuna son zuciya ba.

DiCarlo ta bayyana hakan ne, a taron farko da aka gudanar na kwamitin sulhu na majalisar, kan yadda ake aiwatar da wannan yarjejeniya, tun bayan ficewar Amurka a ranar 8 ga watan Mayu, inda ta ce sau 11, hukumar IAEA ta kasa-da-kasa mai sa ido kan fasahar makaman kare dangi, ta ba da tabbacin cewa Iran na bin ka’idojin da aka gindaya mata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG