Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jarumin Hollywood Alec Baldwin Ya Kashe Mai Shirya Fina-finai Bisa Kuskure


Alec Baldwin
Alec Baldwin

Lamarin ya faru ne yayin da ake daukar fim din "Rust" a kudu maso yammacin Amurka, inda Baldwin din ya kasance babban jarumi a fim din.

Fitacce jarumin Hollywood Alec Baldwin ya harbe wata mai shirya fina-finai har lahira tare da raunata wata darekta bisa kuskure yayin da ake nadar wani fim a jihar New Mexico, kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar.

Lamarin ya faru ne yayin da ake daukar fim din "Rust" a kudu maso yammacin Amurka, inda Baldwin din ya kasance babban jarumi a fim din.

Cikin wata sanarwa da suka fitar, ‘yan sanda a Santa Fe sun ce, Halyna Hutchins da Joel Souza "an harbe su ne lokacin da Alec Baldwin ya ke amfani da bindigar shirya fina-finan. "

An yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen garzyawa da Hutchins, mai shekaru 42 zuwa asibiti, amma ta mutu sakamakon raunukan da ta samu, yayin da Souza, mai shekara 48, an kai ta asibiti a motar daukar marasa lafiya kuma tana samun kulawa.

Jami’an tsaro na bincike akan lamarin, tare da ci gaba da yin tambayoyi ga shaidu, yayin da ya zuwa yanzu, babu wanda aka tuhuma kan lamarin.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG