Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Hillary Clinton Na Amincewa Da Zama Yar Takara


Hillary Clinton
Hillary Clinton

Tace yanzu zabi ya rage gare mu, na kodai mu hada kai domin mu gudu tare mu tsira tare, ko kuma muyi akasi. wadannan dai sune kalaman Hillary a jawabin karshe a daren jiya da ake kammala taron jamiyyar na Democrat a Philadelphia.

‘yar takara wadda take ‘yar shekaru 68 da haihuwa, it ace mace ta farko data taba samun damar a bata damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkasahin tutar daya daga cikin fitattun jamiyyar kasar.

Hilary dai tayi nasara ne bayan datadoke babban aboki karawar ta Sanata Bernie Sanders a zaben da akayi matakin farko na jiha-jiha dama kuma na shugabannin jamiyya.

Sai dai duk da yake Sanders ya nuna gooyon bayan sa ga Hilary a ciki jawabin sa a wajen wannan taron, wani babban kalubale da zata yi karo dashi shine zawarcin magoya bayan Sanders din wadanda suka ce ba zasu goyi bayan ta ba.

Hilary ta yabawa Sanders game da manufofi kamfe dinsa wanda ya mayar da hankali akan halin da matsa suke ciki da kumanuna damuwar sa wajen ciyar da tattalin arziki gaba.

Tace ina fada maka da kyakkyawar murya munji abinda ke damun ka kuma abinda ke damunka muma shi ke damun mu, domin damuwar ka muma damuwar mu ce.

XS
SM
MD
LG