Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Shugaba Buhari Bayan Lashe Zabe


An Baiwa Buhari Da Osinbajo Shaidar Lashe Zabe

Bayan da hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayar da sakamakon zaben da ke nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ‘yan Najeriya suka sake zaba da kuri’un da suka haura miliyan 15.

Hukumar zaben Najeriya INEC ta yi buki a babban dakin taro na kasa da kasa dake babban birnin Abuja, domin mikawa shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa shaidar lashe zaben da aka yi.

Shugaban Najeriya dai da mataimakinsa yanzu zasu jira ranar 29 ga watan Mayu domin a rantsar da su kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Jawabin da shugaba Buhari ya yi wanda yake cikin nutsuwa da nadama, ya yi kira ga ‘yan kasa su bayar da goyon baya domin Najeriya ta ci gaba.

Buhari ya yi na kunshe da abubuwa masu muhimmancin gaske daga alkawurran kawo ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi.

Domin karin bayani kan jawabin shugaba Buhari saurari rahotan Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG