Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jigawa: Ana Yawan Yiwa Yara Mata Fyade


Yara mata

Dr Muhammad Gidado daraktan hukumar tsaro da kare al'umma ta kasa a jihar Jigawa yace daya daga cikin abubuwan da suke fama dashi shi ne masu akidar bata yara kanana mata ta wajen yi masu fyade da dura masu ciki.

Kwana kwanan nan aka kama wani mutum a karamar hukumar Kazaure dan shekaru 32 da ya yiwa wata yarinya karama fyade.

Shi mutumin ya lalata wata yarinya 'yar karama da shekarunta basu kai sha takwas ba.Bugu da kari ya zuba mata ciki.Dr Gidado yace irin wannan abubuwan suna da yawa a jihar.

Yace alkalan jihar suna kokari wajen hukunta wadanda aka samu da laifin yin fyade ko lalata da 'yar yarinya. Ko watan da ya wuce hukumar ta kai wani malami da yake yiwa 'yar makaranta fyade a bayan daki a wata sakandare dake Danzomo. An yanke masa hukumci yana kurkuku.

Dr Gidado yace wasu suna fyde ne saboda bokayensu sun ce idan sun yi lalata da yara kanana zasu warke daga cutar kanjamau. Amma maimakon su warke sai su sake yadawa. Wasu kuma bokayensu sun ce su yi saboda su samu matsayi a gwamnati ko kuma zasu sami kudi. Wasu kuma masifa ce kawai ta fada masu.

Wani da aka kama a Birnin Kudu shekarunsa 28 amma yana lalata da yara 'yan shekaru takwas zuwa tara. Akwai dan shekara 34 da kuma dan 31.Akwai wani kuma a wani kauyen Dutse shi dan shekara 70 ne wanda ya yiwa jikarsa 'yar yarinya karama ciki.

Babbar matsalar dakile fyade tana tattare da dokokin ne. To amma hukumar ta aikawa majalisar dokokin jihar gyara kuma an aiwatar. Yanzu akwai laifin fyade da ka iya ba mutum hukuncin daurin rai da rai. Wasu ma ana iya yanke masu hukuncin kisa.

Don karin bayani ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG