Daliban wata jami'a a jihar Ogun su goma sha biyu, sun mutu a sakamakon hadarin mota a titin Shagamu.
Hatsarin ya faru ne a lokacinda motar su tayi karo da wata babar mota.
Jami'in hulda da jama na rundunar yan sandan jihar Ogun ya tabbarw wakili sashen Hausa Hassan Umaru Tambuwal aukuwar hadarin.
Yace nan take dalibai goma sha biyun suka mutu. Mata biyar da maza bakwai. Daya dalibar data ji rauni an kai asibiti domin yi mata jinya.
Direban babar motar ya gudu, to amma 'yan sanda sunce zasu kama shi.