Accessibility links

JIHAR EDO: Cafke Masu Tsafi da Kashe Mutane


Sabon Babban Sifeton 'Yansandan Najeriya Solomon Arase

Rundunar 'yansandan jihar Edo ta cafke mutane goma sha daya da ake zargin suna sace suna kuma kashe mutane tare da yin tsafi.

Daya daga cikin wadanda aka kama yace shi bai taba kashe kowa ba ko aikata ayyukan ta'addanci ba. Wai ya fito ne daga zantawa da kwamishanan 'yansandan Edo da nufin taimaka masu akan binciken da suke yi aka cafkeshi.

Wadanda aka danko daga jihar Edo suna cikin wata kungiya ce dake da da'awar kare muradun bakar fata. Amma yansanda sun ce suna fakewa ne da hakan domin kashe mutane da aiwatar da ayyukan tsafi.

To saidai Mr Adebowale yace wasu batagari sun karkatar da akalar kungiyar tasu zuwa ga ayyukan tsafi. Amma yace duk tsawon shekaru 17 da yayi a cikin kungiyar bai taba shan jinin wadanda basu ci basu sha ba.

Mataimakin kakakin 'yansandan Najeriya Umar Sheleng ya yi karin bayani.Yace sun fara da jihar Edo amma akwai wasu jihohin a kudancin kasar kamar irinsu jihohin Akwa Ibom da Rivers da suka yi kamarin suna a ayyukan tsafi da kashe mutane. Yace a Edo an kamo wasu mutane kuma an samu abubuwa a hannunsu, kamar su makamai, hotunan mutanen da suka rubuta R.I.P., wato ko sun kashesu kokuma suna shirin kashesu..

Ga rahoton Nasiru El-Hikaya.

XS
SM
MD
LG