Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar Ta Kulla Yarjejeniyar Kasuwanci da Kamfanin Dantata


 Gwamnan Jihar Maradi, Malam Zakari Umaru a tsakiya
Gwamnan Jihar Maradi, Malam Zakari Umaru a tsakiya

A taron masu ruwa da tsaki akan harkokin kasuwanci da gwamnan jihar Maradi ya kira ya shaidawa duniya yarjejeniyar da jiharsa ta yi da kamfanin Dantata na Najeriya akan gina masana'antu guda uku.

Malam Zakari Umaru ya kira taron manema labarai ne domin bayyana wa jama'a yarjejeniyar da jihar ta kulla da kamfanin Dantata da za ta zama da alfanu ga jihar.

A cewar gwamnan, Malam Zakari Umaru, jiharsa ta na da hulda da gwamnatin jihar Kano. Sun gane cewa akwai 'yan kasuwa masu karfi a jihar ta Kano da suka yi fice a Najeriya da kasashen waje. Dalili ke nan, inji gwamnan, suka tunkari kamfanin Dantata suka bayyana masa irin arzikin da jihar Maradi ke dashi.

Cikin abubuwan da jihar Maradi ta shimfida wa kamfanin Dantatan, ya zabi abubuwa uku da zai yi. Na daya zai kafa kamfanin hada takin zamani. Na biyu zai bude kamfanin hada abincin dabbobi. Abu na uku kamfanin zai dinga sarafa naman da ake yankawa ya mayar dashi tamkar kankara cikin awa daya ya kaishi kasashen waje da jiragen sama.

Kafa wadannan kamfunan uku zasu samar ma tasa ayyukan yi, su rage zaman kashe wando. Kazalika za'a samu ci gaban tattalin arziki a fadin kasar gaba daya, inji gwamnan.

Wasu matasan da aka zanta dasu sun nuna farin cikinsu saboda zasu samu ayyukan yi. Baicin hakan darajar Maradi za ta karu a duk fadin kasar Nijar tare da daukaka Nijar kanta cikin kasashen duniya, a cewar matasan.

Ga rahoton Mani Chiaubu da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG