Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Niger: 'Yan sara suka sun jikatta mutane fiye da 10 a Kontagora


 Sarkin Kontagora, Saidu Namaska
Sarkin Kontagora, Saidu Namaska

Wasu da ake kyautata zato 'yan sara suka ne sun afkawa wani masallaci a unguwar Dadinkowa dake cikin garin Kontagora na jihar Niger inda suka rika dukan mutane tare da sararsu har suka jikatta kimanin 12 da yanzu rayukansu na hannun Allah

Kimanin mutane goma ne ke kwance rai kwakwai mutu kwakwai a wani asibitin gwamnatin jihar Niger dake garin Kontagora.

Rahotanni na cewa wasu matasa ne da ake kyautata zaton 'yan sara suka dauke da makamai suka aukawa mutane bayan sun kammala sallar isha'i a unguwar Dadinkowa dake cikin garin Kontagoran.

Malam Murtala Abdullahi kwamandan kungiyar hisbah dake taimakawa wajen tabbatar da tsaro a garin, ya yiwa Sashen Hausa karin bayani ta waya. A cewarsa wasu ne suka zo da sanduna da adduna kuma duk wanda suka gani sai su kama sara. Ya ga wani da aka sare masa hannu da cinya. Har wani dan gidansa shi ma an sare masa kafa. Ya ce da ya je ofishin 'yan sanda ya shigar da rahoto, sai aka fada masa an wuce da wasu asibiti saboda haka ya bisu. A asibitin ya ga mutane goma, daga baya kuma aka kara kawo wasu biyu.

Hakazalika wani malami a unguwar da shi ma lamarin ya rutsa da dalibansa ya yi karin bayani. Malam Aliyu Muhammad Sani Adarawa, ya ce an sassare dalibansa biyu. Jinin daya ma har ya kare saboda haka ana neman samar masa jini.

Mai unguwar Dadinkowan Malam Bashir Muhammad, ya ce ya zuwa shadayan daren Lahadi kura ta lafa.

Duk da cewa kakakin 'yan sandan jihar DSP Abubakar Dan Inna bai dauki wayarsa ba lokacin da Sashen Hausa ya nemeshi, amma wani babban jami'in 'yan sandan da bai so a ambaci sunansa ba saboda wai ba huruminsa ba ne, ya tabbatar da aukuwar lamarin har ma ya ce suna rike da mutane hudu da suke zargin suna da hannu cikin aika aikar.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG