Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Osun Za Ta Kafa Kwamiti Don Bincikar Rikicin Ile-Ife


Gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola

Gwamnatin jihar Osun ta ce nan ba da dadewa ba za ta kafa kwamitin binciken musabbabin rikicin Yarabawa da ‘yan Arewa a garin Ile-Ife wanda ya yi sanadiyar rayukan mutane da yawa da kuma lalata dukiyoyi.

Gwamna Rauf Aregbesola, ya bayar da tabbacin kafa kwamitin ne unguwar Sabo Ile-ife, lokacin da ya raka tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yayin da ya kai ziyarar jajantawa ‘yan Arewa game da abin da ya faru da kuma asarar da suka yi a rikicin.

Aregbesola, ya ce a matsayinsa na gwamna zai kafa kwamitin da zai binciko sanadiyar tashin hankalin da ya faru da nemo masalaha da kuma taimakawa mutanen su rage radadin asarar da su ka yi. Gwamnan ya ce jami’an tsaro sun damke wasu mutane 20 da aka zargi da laifin kisa da lalata dukiyoyi.

Da yake magana da manema labaru Sanata Kwankwaso, ya ce yazo ne biyo bayan rigingimun da suka faru a garin Ile-ife wanda yanzu haka an riga an shawo kan su, yasa ya kawo ziyara domin jajantawa ‘yan Arewan da iftila’in ya afkawa.

Haka kuma ya yi alkawarin cewa gidauniyarsa ta Kwankwasiya za ta taimakawa mutanen da suka yi asara.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG