Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Za Ta Binciki Zarge-zargen Take Hakkin Bil Adama


buratai

Rundunar sojan Najeriya ta kaddamar da kwamitin da zai binciki zarge-zargen take hakkin bil Adama da wasu kungiyoyin rajin kare hakkin ‘dan Adam ke yi wa sojoji.

Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya kaddamar da wani kwamiti mai karfin gaske da zai binciki zargin da kungiyoyin kare hakkan bil Adama ke yi wa sojoji. Inda ya nuna cewa suna sane da mutane da kungiyoyin da ke zargin sojoji da yiwa ‘yan cin bil Adama karan tsaye.

Rahotan kungiyar Amnesty International ya zargi jam’an soja da yin kisan gilla ga masu rajin kafa ‘kasar Biafra, da kuma take hakkin ‘dan Adam na ‘yan Boko Haram din da aka kama. Cikin zarge-zargen akwai kashe mutum ba tare da dalili ba, da kame-kamen mutane ba tare da ‘ka’ida ba, har da azabtar da mutane da kuma batar da su.

A cewar Buratai, akwai bukatar gudanar da bincike na tsakani da Allah don gano gaskiyar lamari, wanda hakan yasa aka kwamitin bincike na musamman.

Rundanar sojan Najeriya ta ce wannan kwamiti ba zai binciki korafin da hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya, ko binciken da wasu gwamnatocin jihohi suka yi.

A cewar shugaban sabon kwamitin binciken major janar A.T Jibrin mai ritaya, ya ce za su yi bulaguro zuwa dukkan gurare, kuma za su gayyaci duk masu abin fada a cikin wannan batu don tabbatar da bin diddigin magana daga tushe. Kuma ya ce za su yi gaskiya da adalci.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG