Accessibility links

Oyo: 'Yan Fansho 500 Suka Rasu Suna Jiran Biya


Maso karbar fansho

Masu karbar fansho a jihar Oyo sun ce sama da mutanensu 500 suka mutu sakamakon rashin samun kudaden fanshonsu.

Masu karban fanshon sun furta hakan ne jim kadan bayan sun kammala wani taron gaggawa a birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar.

Haka ma masu karban fanshon sun baiwa gwamnatin jihar wa'adin kwanaki bakwai ta biyasu hahhohinsu na watanni biyar ko kuma su shiga yin zanga-zangar sai baba ta gani.

Mr. Olusegun Abatan sakataren kungiyar 'yan fansho a jihar Oyo yace idan gwamnatin jihar bata biyasu kudinsu ba daga watan Janairu na wannan shekarar zasu shiga zanga na har illa mashaallahu. Yace sun dadae suna yiwa gwamnatin hakuri amma bata nuna ko ta damu da irin halin da suke ciki ba.

Da yake mayarda martani a madadin gwamnat akan wa'adin kwanaki bakwai da 'yan fanshon suka ba gwamnati, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Mr. Soji Oniyide cewa yayi ba wai gwamnatin bata son ta biya kudin fansho ba ne akwai wani shirin biyan hakkokinsu a kasa.

To saidai Mr. Oniyide ya bukaci 'yan fanshon da su kara hakuri. Yace nan ba dadaewa ba za'a biya masu bukatunsu.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

XS
SM
MD
LG