A wani bincike da ta gudanar a shekara ta 2016, hukumar lafiya a Najeriya ta ce an samu adadin yaran da suka kamu da cutar kyanda 3, 905 a jihohi hudu da suka fi fuskantar cutar.
Jihohin sun hada da Borno da ke da yara 846, Yobe mai yara 2510, sai Adamawa da ke da yara 273 inda Gombe ke da yara 276.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO da hukumomin lafiya na Najeriya na karfafa batun rigakafi musamman ma a sansanonin ‘yan gudun hijira ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar.
Bayan haka mata ma idan sun taru a asibitoci kan samu wayar da kai kan muhimmancin rigakafin don kare yaransu daga cututtuka shida masu kisa ciki har da cutar kyanda.
An samu wayewar kai kan kin jinin rigakafi musamman a Najeriya in aka debe sassan da ake da kalubalen tsaro na arewa maso gabas.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 27, 2023
Dalilin Da Ya Sa PDP Ta Dakatar Da Ayu
-
Maris 24, 2023
Mun Turawa Bankuna Kudi - CBN
-
Maris 24, 2023
Kotu Ta Jaddada Nasarar Adeleke A Zaben Gwamnan Osun