Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohin Najeriya 3 kadai Za Su Iya Biyan Albashi Bayan Zabtare Kudaden Kananan Hukumomi - BudgIT


Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna
Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna

Kungiyar BudgIT ta bayyana cewa jihohin Najeriya 3 ne kadai daga cikin 36, za su iya biyan albashi bayan da gwamnatin tarayya ta cire Naira biliyan 172 daga asusun kananan hukumominsu.

Babu tabbas a kan batun biyan albashin ma’aikatan kimanin jihohi 33 saboda shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na cire kudadde daga asusun kananan hukumomi domin fara biyan kudi dala miliyan 418 ga masu ba da shawara da ke zaman kansu kan tallafin asusun Paris Club.

Kudadden wanda kwatankwacin Naira biliyan 172 ya sanya jihohi da kananan hukumomi yin adawa da matakin na gwamnatin tarayya.

A cikin rahoton ta mai taken “Yanayin da jihohi ke ciki”, BudgIT, wata kungiya da ta himmatu ga aikin tabbatar da yin abubuwa a bayyane game da harkokin da suka shafi kudaden gwamnati, ta ce gwamnatocin jihohin Najeriya uku da suka hada da Legas, Ribas da Akwa Ibom ne kawai za su iya daukan nauyin kula da ayyukan jihohinsu su ba tare da rabon da su ke samu daga gwamnatin tarayya ba.

Tun da dadewa ne kungiyar gwamnonin Najeriya da sauran jama'a kasar suka yi ta matsin lamba don a dakatar da biyan kudaden da ake zargin ba daidai ba ne, ga masu ba da shawara dake zaman kansu.

Saidai a wani lamari da ba’a fahimta ba tukunna shi ne, kasa da wata guda bayan umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, ma'aikatar kudi, kasafi da tsare -tsare ta kasa ta fara cire kudaden da za'a biya masu ba da shawarar nan da ake kiki-kaka a kan su.

Babban sakataren ma’aikatar kudi ta tarayya, ya fada wa taron kwamitin asusun rabon kudi na tarayya, wato FAAC a ranar juma’a cewa an fara cire kudaden don biyan masu ba da shawarar.

Wannan bayanin bai yiwa gwamnonin jihohi dadi ba wanda daga baya suka ki yin magana a kan kudaden shiga na watan Oktoban shekarar 2021 har sai gwamnatin tarayya ta yi gamsashen bayani kan kudadden da ta ce ta fara cirewa daga asusun kananan hukumomi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ana iya tunawa, a shekarar 2006 ne gwamnatin tarayya ta biya dala biliyan 12 don samun biyan bukatar yafe bashin dala biliyan 18 na asusun Paris Club na masu ba da bashi na duniya.

Sai dai sakamakon biyan kuɗin kai tsaye daga kudaden shigar tarayya, gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da ba ta bin bashin Paris Club suka nemi gwamnatin tarayya ta mayar mu su kudadden.

Lamarin da ya kai ga wasu masu ba da shawara suka fito don neman nasu kaso na kudaden da aka dawo dasu a matsayin biya kan ayyukan da suka yiwa jihohi da kananan hukumomi.

XS
SM
MD
LG