Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohin Zamfara, Kano Sun Rufe Makarantun Kwana


Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle.
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle.

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe daukacin makarantun kwana da ke jihar biyo bayan sace dalibai sama da 300 da aka yi.

Da sanyin safiyar ranar Juma’a ‘yan bindiga suka yi awon gaba da daliban makarantar sakandaren Jangebe da ke karamar hukumar Talatan Mafara.

Gwamna Bello Matawalle ne ya sanar da wannan mataki na rufe makarantun a wani jawabi da ya yi kai-tsaye ga al’umar jihar ta kafar talbijin a ranar Juma'a.

“Idan muka hada kanmu ne kawai za mu iya yakar wannan babban kalubale. Bai kamata banbancin siyasa ko wani abu ya janyo cikas a yakin da muke yi da matsalar tsaro ba.” Matawalle ya ce cikin yanayi na alhini.

Gwamnan ya yi kira ga al’umar jihar da su “kwantar da hankalinsu, su kuma guji wadanda suke so su yi amfani da wannan lamari don cimma burinsu,” yana mai mika jajensa ga iyaye da 'yan uwan daliban.

Rundunar ‘yan sanda jihar ta Zamfara ta ce dalibai 317 ‘yan bindigar suka sace.

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

A jihar Kano da ke da tazarar kilomita sama da 300 wacce har ila yau take makwabtaka da jihar ta Zamfara, hukumomi sun ba da umurnin rufe wasu makarantun kwana guda 10.

Wata sanarwa da Kwamishinan Ilimin jihar Muhammad Sunusi Kiru ya fitar, ta ce an rufe makarantun Mariana, Sule Science College Gaya, Makarantar sakandaren mata ta Kachako da sauransu, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

Dukkan wadannan al’amura na faruwa ne kwanaki 9, bayan da wasu 'yan bindigar suka yi awon gaba da dalibai da malamai a makarantar sakandare ta Kagara a jihar Neja, wadanda har yanzu ba a sako su ba.

Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fuskantar ukubar 'yan bindiga baya ga Katsina da Sokoto.

XS
SM
MD
LG