Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Addu'o'i Ga Wadanda Suka Mutu a Harin Texas


Lokacin da ake gudanar da addu'o'i ga wadanda suka mutu a harin Santa Fe na jihar Texas a Amurka

Jama'ar yankin Santa Fe da wani dan bindiga ya kai hari, na ci gaba da jimami da addu'o'i ga mutane 10 da suka mutu daga harin na makarantar sakandaren da ke jihar Texas a Amurka.

Al’umar yankin Sante Fe da ke Jihar Texas na ci gaba da jimamin harbin-kan-mai-uwa-da-wabi da ya halaka mutane goma, mafi aksarinsu dalibai, a wata makarantar Sakandare.

Ya zuwa yanzu hukumomin jihar sun ce mutane 13 ne suka ji raunuka baya ga wadanda suka mutu, yayin da a jiya adadin wadanda suka jikkatan ya tsaya a goma.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin, Randy Weber, yayin wani taro da aka yi a jiya Asabar, ya ce za su farfado daga wannan musiba, za kuma su ci gaba da kauna tare da aiki da junansu.

Jami’an tsaro a jihar ta Texas sun tuhumi wani matashi mai shekaru 17, mai suna Dimitrios Pagourtzis da laifin wannan hari.

Shugaban Amurka Donald Trump yayin wani takataiccen jawabi da ya yi bayan harin, ya ce "gwamnatinmu za ta yi iya baki kokarinta, wajen kare dalibai da makarantu, mu kuma kawar da makamai daga hannun wadanda suke barazana ga kansu da kuma sauran jama’a.

Gwamnan jihar ta Texas, Greg Abbot, ya ce makamai biyu aka yi amfani da su a harin, daya, wata babbar bindiga ce, ta biyun kuma karama ce, kuma duk na mahaifin matashin da ya kai harin ne.

Sai dai ya ce babu bayanai da ke nuna cewa, ko mahaifin matashin yana sane dansa ya dauki bindigogin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG