Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Kasashen Waje Sun Fara Jigila Daga Kaduna


Irin jiragen dake tashi da sauka a Kaduna
Irin jiragen dake tashi da sauka a Kaduna

Jiragen kasashen waje sun fara jigila daga filin tashin jiragen sama dake Kaduna bayan rufe na Nnamdi Azikwe na Abuja da hukumomi suka yi domin a gudanar da gyare-gyare a zirin da jirage ke sauka da tashi.

Jirgin kasar Habasha na Ethiopia Airline shi ne na farko da ya kammala lodin mutane ya kuma tashi daidai karfe dayan rana agogon Najeriya daga Kaduna zuwa Addis Ababa.

Ministan harkokin jiragen sama Sanata Hadi Sirika shi ya kaddamar da fara aiki da tashar yau Laraba a garin Kaduna.

Ministan ya ce yin amfani da tashar Kaduna ba zai wuce na tswaon makwanni shidan da aka kayyade ba.

Ya kuma ce abun da wasu suka ce ba zai yi wu ba yau gashi ya faru yana mai cewa abubuwan da aka sa a tashar suna aiki daidai.

Dangane da wasu kamfanonin kasashen waje da suka nuna shakkun zuwa, ministan ya ce tunda an fara tashi a Kaduna suma za su bi sahu.

Domin sauraron cikakken rahoton sai a dannan maballin fara sauraron sautu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG