Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Tashar Saukar Jirage Ta Abuja


Tashar saukar jirage ta Abuja.
Tashar saukar jirage ta Abuja.

Yanzu haka ‘yan Najeriya matafiya a ciki da waje, sun kuduri aniyar fuskantar matsalolin da ba a rasa ba domin kulle tashar jirgin sama ta babban birnin Abuja.

Mahukuntan kasar suna sa ran cewa babbar tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja, za a daina aiki cikin ta, wato sauka da tashin jirage har na tsawon makwanni shida domin gyaran titin da jirage ke tashi da sauka.

Jami’an sun ce ba yadda za a iya gudanar da aikin ba tare da rufe tashar ba gaba dayan ta.

Yanzu ya zama wajibi ga masu tashi da sauka ta tashar da aka kulle su sauka a karamar tashar dake birnin Kaduna wadda ba ta kai girman ta Abuja ba, wanda kuma daga Abuja zuwa kaduna tafiyar sa’oi uku ne, kana ana korafin rashin tsaro a tsakanin biranen biyu.

Sai dai gwamnatin kasar ta yi alkawarin girke jami’an tsaron hadin gwiwa wanda zai kunshi sojoji da ‘yan sanda, da za su rika sintiri akan hanyar.

Akwai rahotanni dake nuna cewa wasu jiragen kasa da kasa tuni suka tirje suka ce ba za su sauka a wannan tashar jirgin ba.

Rufe wannan tashar ba wai matafiya ne kadai za su ji a jikin su ba, hatta ma’aikata da masu sana’ar da suka hada da masu sayar da abinci ko kuma hayar motoci za su kwashe kwanaki ba tare da wani abin yi ba.

Dama dai matafiya masu amfani da wannan tashar jirgin saman sun dade suna kokawa kan rashin kyawun kayayyakin da ake amfani da su a tashar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG