Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen saman Amurka na shawagin sintiri a fadin Afirka


Sakataren Tsaron Amurka, Leon Panetta
Sakataren Tsaron Amurka, Leon Panetta

Jaridar Washington Post ta ce Amurka ta bude kananan filayen jiragen sama a sassan Afirka

Jaridar Washington Post ta ce Amurka ta bude kananan filayen jiragen sama a sassan Afirka don sa ido kan kungiyoyin ta’adda.

Jaridar, wadda ta ambaci wasu jami’an Amurka da na Afirka a matsayin majiyoyinta, ta ce an bude irin wadannan filayen jirgin wajen 12 a wasu kasashe ciki har da Burkina Faso da Uganda da Habasha da Djibouti da Kenya da Seychelles.

Jaridar ta Post ta ce amaimakon amfani da jiragen da bas u da matuka, ana amfani ne da kananan jirage wajen shawagin sa ido din – akasari sanfurin PC-12s masu kananan injina da matuki kawai ciki.

Rahoton ya ce jiragen na dauke da kamarorin daukar hotunan bidiyo, da kuma na’urar jin dumin tafiyar abu mai rai, wadda kuma ke iya cabko sautin sakonni da na wayar selula.

Kakakin Dakarun Tsaron Kenya, Kanar Cyrus Oguna, ya karyata labarin kasancewar filayen jiragen saman Amurka a Kenya.

XS
SM
MD
LG