Accessibility links

Jiragen Yakin Isra'ila Sun Kai Hari Gaza

  • Aliyu Imam

Hayaki yake tashi a yankin zirin Gaza.

Jiragen saman yakin isra’ila sun kai hari Zirin Gaza inda suka kashe Falasdinawa uku wadanda Isra’ila tayi zargin ‘yan tsagera ne.

Jiragen saman yakin isra’ila sun kai hari Zirin Gaza inda suka kashe Falasdinawa uku wadanda Isra’ila tayi zargin ‘yan tsagera ne dake harba rokoki zuwa Isra’ila a kwanaki uku a jere.

Jami’an kiwon lafiya falasdinawa sun bayyana cewar hare-haren jiragen saman yakin Isra’ial an kaisu ne jiya lahadi, daga cikin wadanda suka halaka a dalilin hare-haren harda wani dattijo mai shekaru sittin a duniya da kuma yaro mai shekaru goma sha biyu harin ya sme shi a kan hanyarsa ta zuwa makaranta a garin Jebaliya na Zirin Gaza.

Isra’ila tace jiragen saman yakinta suna auna wuraren da ‘yan tsagera ke jan daga ne daga inda suke harba rokoki fiye da Talatin kan Isra’ila.

XS
SM
MD
LG