Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Mai Amfani Da Karfin Rana Ya Tashi A karo Na Farko


Jirgi mai amfani da karfin rana.
Jirgi mai amfani da karfin rana.

A Karo na Farko jirgi mai amfani da karfin rana ya tashi daga jihar California.

Jiya jumma’a a karo na farko a tarihi wasu matuka jirgin sama su biyu ‘yan kasar Swisszeland, suka tashi daga jihar California a wani yunkurin ratsa kasar da wani jirgi da yake aiki da karfin rana.

Jirgin wanda yake da fukafiki na jirgi samfirin 747, amma nauyinsa bai wuce na motar-shiga ‘yar tsaka tsaki ba. Baturan jirgin su suke tattarawa su kuma adana karfin rana, domin jirgin ya sami sukunin tashi dare da rana. Sai dai jirgin baya wuce tafiyar kilomita 69 ko wani sa’a daya, kuma kujerar matuki daya tal jirgin yake da shi,wanda hakan ya tilasta ya rinka tsatstsayawa domin hutu.

Borschberg suna shirin tsayawa a Phoenix, da Dallas, da St.Louis da Washimngton kamin su sauka a birnin New York cikin watan gobe.

Piccard da Borschberg suna kallon balaguronsu cikin wannan jirgi a matsayin mutanen nan na farko da suka fara tuka jiragen sama a duniya. Sun amince lallai ba a kai ga lokacin fara amfani da irin wannan jirgi mai amfani da karfin rana domin kwasar fasinja ba, amma suna fatan hakan zai kai taimaka wajen cigaba da nazarin hanyoyin inganta makamashi da jirage zasu yi amfani da shi.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG