Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Da Ya Yi Hatsari Yana Shirin Zuwa Neman ‘Yan Makarantar Kagara Ne – Sojojin Najeriya


Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Oladayo Amao (Hoto: NAF Twitter)

Rundunar sojin saman Najeriya na ci gaba da yin karin haske dangane da hatsarin da jirgin samanta ya yi wanda ya halaka mutum bakwai.

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jirginta da ya fadi ya halaka mutum bakwai dake cikinsa a Abuja babban birnin kasar, yana shirin zuwa yin shawagin tattara bayanan sirri ne a lokacin da ya fadi.

Wata sanarwa dauke da sa hannun darektan yada labaran rundunar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, wacce aka wallafa a shafin Twitter, ta nuna cewa jirgin mai suna Beechcraft KingAir kirar B350I (NAF 201) ya samu matsalar injin ne yana kuma hanyar komawa filin tashin jirgin saman a Nnamdi Azikwe domin yin gyara a lokacin da ya fadi.

Jirgin ya fadi ne, “yayin da yake shirin zuwa aikin tattara bayanai a jihar Neja da kewaye a kokarin da ake yi na kubutar da daliban makarantar gwamnatin ta Kwalejin Kagara da aka yi garkuwa da su.” Sanarwar ta ce.

Sunayen Sojojin Saman Da Suka Mutu a Hatsarin

A halin da ake ciki rundunar sojin saman ta Najeriya ta ce ta sanar da iyalan da magadan wadanda wannan hatsari ya shafa kuma har ta fitar da sunayensu tana mai nuna alhininta bisa wannan ibtila’I kamar yadda sanarwa ta nuna.

Sunayen mamatan sun hada da:

- Flight Lieutnant Haruna Gadzama (Kyaftin)

- Flight Lieutenant Henry Piyo (Mataimakin matukin jirgi0

- Flying Officer Michael Okpara (kwararren a fannin tsara ayyukan sama)

- Warrant Officer Bassey Etim (Kwararre)

Flight Sergeant Olasunkanmi Oluwunmi (kwararre)

Sergeant Ugochukwu Oluka (Kwararre)

- Aircraft Adewale Johnson (Kwararren makaniken jirgi)

Amurka Ta Mika Sakon Ta’aziyya Ga Najeriya

Bayan aukuwar wannan hatsari, ofishin jakadancin Amurka na Najeriya, ya mika sakon ta’aziyya tare da taya iyalan mamatan da ‘yan Najeriya alhinin wannan rashi.

“Amurka na mika sakon ta’aziyya ga rundunar sojin saman Najeriya, (@NigAirforce) iyalan mamatan da ‘yan Najeriya bisa wannan rashi da ya faru a hatsarin jirgin na yau.” Sanarwar wacce ofishin jakadanci ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce

XS
SM
MD
LG