Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Da Yayi Batan Dabo Ya Dawo


Aircraft

Jirgin saman jihar Bauci da ya makale a kasar Morocco ya dawo gida.

Jirgin saman mai daukar mutane 54 ya sauka ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauci a karkashin jagorancin matukin jirgi Captain Moyo.

Mataimakin Gwamnan jihar Bauci Alhaji Nuhu Gidado sardaunar Jamaare shine ya karbi jirgin.

‘’Yau ta tabbata ga jirgi ya sauka a Bauci wadan su yan a bata tsakani ne, cewa muka yi jirgin mu da yake kasa baya ciki Najeriya amma yana Morocco aka dauki wannan, wani dan jarida yaje ya rubuta cewa jirgin da aka sace daga Bauici kamar wani kwalin ashana yau muna alfahari da dawo da wannan jirgin, saboda jirgin da aka saye shi yau shekara tar aba a miore shi ba, muka ce dole jirgin nan ya dawo kuma mutane su anfana daga wannan jirgin.’’

To kamar wace yarjejeniya ce kukakulla da wannan kanfanin a halin yanzu?

‘’Dama akwai yarjejeniya tsakanin su da gwamnati data shude an sayi jirgi kuma basu suka saya ba zamanin Ahmed Muazu aka sayi jirgin nan, kuma su suka zo suka gaje shi amma rikon sakainar kashin da aka yi, sabanin da aka samu Kenan muka ce ba zamu yadda ba jirgi ya dawo gida a ganshi sabo da yanzu lissafin da muka yi wurin miliyan dari takwas aka kashe akan wannan jirgi kuma bai samo miliyan dari 2 ba ko 3 ba’’.

Captain Mayo shinemanajan kanfanin Overland wanda jirgin ke hannun su.

Ga Abduwahab Mohammed da Karin bayani 3’06’

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

XS
SM
MD
LG