Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama


Ana cigaba da samun bayanan yadda rayuwa take a duniyar sama.

Wani jirgin jigila na hukumar sama jannatin Amurka (NASA) ya isa tashar sararin samaniya ta kasa da kasa (ISS) jiya Litinin, dauke da sama da kilogram 3,600 na kayan bincike da kayayyaki zuwa dakin binciken na sararin samaniya.

Jirgin, wanda kamfanin Northrop Grumman ya kera, an daure shi a sashin tashar ISS mai fuskantar Duniya jim kadan da isarsa.

Baya ga kayan amfani na tashar sararin samaniya, kayayyakin da jirgin ke dauke da su, sun hada da kayan aiki don gudanar da binciken kimiyya don kirkirar wata fasaha da za a iya amfani da ita wajen magance cutar ido, da samar da kwamfutocin da zasu yi aiki a sararin sama, da kuma gano dalilin raunin tsokar idanu da 'yan sama jannatin suke fuskanta a sararin samaniya ta hanyar amfani da kananan tsutsotsi.

XS
SM
MD
LG