Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin leken asiri: Iran ta yi watsi da bukatar Amurka


Hoton jirgin saman Amurka da ke hannun Iran
Hoton jirgin saman Amurka da ke hannun Iran

Iran tayi watsi da bukatar Amurka ta neman maida mata jirgin

Iran tayi watsi da bukatar Amurka ta neman maida mata jirgin saman ayyukan leken asirin da babu matuki a cikinsa. Jirgin saman da Iran tace ta kakkabo daga sama a kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan a farkon wannan watan.

A Talatar da ta gabata ce aka ji mukadashin Ministan tsaron Iran, Janaral Ahmad Vahidi, yana cewa yanzu wannan jirgin saman yakin ya zama mallakin kasar Iran.

Haka kuma anji gidan rediyon kasar Iran yana ambaton mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ramin Mehmanparast, yana fadin cewa tura wannan jirgin saman leken asirin da Amirka tayi, keta ka’idar matakan tsaron kasar ne don haka kamata yayi Amirka ta nemi gafara.

Yace ya kamata, Amirka ta san cewa matakin da ta dauka keta ka’idar sararin samaniyar Iran ne, kuma yana iya janyo barazana ga matakan tsaro da zaman lafiya a duniya.

Aika Sharhinka

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG