Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasar Panama Manuel Noriega Ya Koma Gida


Wani tsohon hoton janar Manuel Noriega ya na magana da 'yan jarida a Panama a cikin watan mayun shekarar 1989, jim kadan kafin Amurka ta kai mar farmaki ta tumbuke shi daga karagar mulki

Tsohon shugaban mulkin sojan zai fuskanci hukumce-hukumce har 3 da aka yanke masa a cikin kasar Panama

Tsohon shugaban kasar Panama, Manuel Noriega, ya koma gida a bayan da ya shafe shekaru fiye da 20 a gidajen kurkukun Amurka da Faransa.

Noriega ya isa Panama da maraicen lahadi, a bayan da aka mika shi ga kasarsa daga hannun Faransa, wadda ta daure shi bisa zargin batar da sawun kudaden haramun.

A yanzu tsohon shugaban mulkin sojan zai fuskanci hukumce-hukumce har uku da aka yanke masa a cikin kasar Panama kan kashe abokan adawar siyasarsa, ciki har da sare kan Hugo Spadafora da aka yi a shekarar 1985.

Noriega yayi mulki irin na kama-karya a kasar dake tsakiyar nahiyar Amurka a shekarun 1980, a lokacin da yake yiwa Hukumar leken asirin Amurka ta CIA aiki. Amma kuma Amurka da kanta ta kai farmaki ta tumbuke shi daga kan karagar mulki a shekarar 1989.

A bayan da aka daure shi a kurkuku a nan Amurka bisa tuhumar safarar muggan kwayoyi, an mika Noriega ga kasar Faransa wadda ita kuma ta daure shi kan batar da sawun kudaden haramun.

Noriega, mai shekaru 77 da haihuwa, ya cancanci daurin talala a gidansa a saboda yawan shekaru.

A tsawon shekarun da Noriega yayi yana dan leken asirin Amurka, ya hada kai da gungun safarar muggan kwayoyi ta Medellin Cartel a kasar Colombia, inda ya rika batar da sawun kudaden kwayar kungiyar, ya kuma maida kasar Panama ta zamo zangon safarar kwayoyin a kan hanyarsu ta zuwa kasashen waje.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG