Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Ruwan Australia Mara Matuki Zai Binciko Baraguzan Jirgin Malaysia da Ya Bace


Jirgin Malaysia da ya bace

Yau fiye da shekaru biyu ke nan da jirgin Malaysia dauke da fasinjoji fiye da dari biyu ya bace akan hanyarsa daga Kuala Lumpur zuwa Beijing kuma duk cigiya da bincike binciken da aka yi sun cutura

Kasar Australia tace za’a yi amfani da jirgin karkashin ruwa mara matuki, wajen neman jirgin saman Malaysia mai lambar tafiya 370 da ya bace shekarun baya.

Hukumar kare Haduran Sufuri ta Autralia ta fadi yau Laraba cewa zata saka jirgin karkashin ruwa mara matukin a daya daga cikin jiragen ruwa masu binciken teku mai zurfi don ya taimaka wajen nazarin baraguzai da dama da aka gano a binciken da ya gabata, ganin da alamar daga abubuwan da dan adam ya kera ne baraguzan su ka fito.

Za’a gudanar da bincken ne daura da gabar yamma ta Australiar, inda jami'an bincike suka ce sun gano tarkace sama da 20 masu alaka da kerarren abu, wadanda ke bukatar karin bincike.

Jirgin saman Malaysia ya bace ne sama da shekaru biyu da suka gabata ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2014, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Beijing daga Kuala Lumpur. Fasinjoji 239 ne suke cikin jirgin.

Duk da neman da akai tayi a gabar ruwan Autraliar da kewaye, inda masu bincike ke kyautata zaton nan ne jirgin ya fadi, ba’a ga alamar jirgin ko mutanen dake ciki ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG