Accessibility links

'Yan bindiga sun kaiwa garin Madagali hari da sanyin safiyar alhamis.

'Yan bindiga sun kaiwa garin Madagali hari da sanyin safiyar alhamis,inda suka yiwa gari diran mikiya akan macina da motoci.

A wannan harin da suka kai sun kona wani sashe na sakatariyar gudumar raya kasa dake Madagli.

‘Yan bindigan sun kashe mutane biyu farar hula da soja sun kuma yi awon gaba da motoci soja guda biyu.

A wani matakin maida martani jirgin sama na sojojin Najeriya daya kawo dauki ya jefa bom akan ‘yan bindigan da suka kai harin wada ya shafi wani coci.

Shugaban karamar hukumar Madagali Mr. James Watarda ya tabbatar da wannan lamarin ya kuma yi kira da a kawo masu dauki.
XS
SM
MD
LG