Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Soja Mai Saukar Ungulu Yayi Hatsari A Afghanistan


Afghanistan

Wani jirgin soji mai saukar ungulu ya yi hadari a Arewacin kasar Afghanistan kuma ya hallaka mutane Bakwai dake cikinsa.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Dawlat Waziri ya tabbatar da wannan hatsarin, yace matattun sun hada da sojojin Afghanistan guda uku da ma’aikatar jirgin su hudu.

Waziri ya dora laifin hatsarin akan matsalar na’ura na wannan jirgin kirar Rasha, samfurin Mi 17, wanda ya fadi lokacinda yake jigilar kayan taimako ga sojojin Afghanistan.

To amma mayakan Taliban suna ikirarin sune suka harbor jirgin mai saukar ungulu, suna cewar jirgin ya tasar ma wani sansani da su yan Taliban din suka kewaye sojoji 200 sama da mako daya.

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG