Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Talata Aka Kammala Zaben Liberia da Zai Samar da Sabon Shugaban Kasa


Masu jefa kuri'a suna jira a fara zabe a Liberia
Masu jefa kuri'a suna jira a fara zabe a Liberia

An rufe rumfunan zabe a Liberia, inda masu kada kuri’a a jiya Talata suka jefa kuri’unsu domin zaben shugaban kasa, zaben da zai zamanto na farko cikin shekaru 70, wanda za a mika ragamar mulki daga wata gwamnati zuwa wata, a karkashin mulkin Dimukradiyya a kasar wacce ke yammacin Afirka.

Masu kada kuri’a da yawansu ya kai miliyan 2.1, sun yi zaben wanda zai gaji shugabar kasar Ellen Johson Sirleaf, mace ta farko da ta zama shugabar kasa a nahiyar Afirka, wacce kuma ta taba samun lambar yabo ta “Nobel” ta zaman lafiya.

Sirleaf bata takara a zaben ne saboda ta kammala wa’adin mulkin biyu na shekaru shida-shida, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta Liberia ya tanada.

Nan da makwanni biyu dai ake sa ran fitar da sakamakon zaben.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta kwatanta zaben a matsayin wanda ta ce ya kai wani muhimmin mataki da za a mika mulki daga wata zababbiyar gwamnati zuwa wata cikin lumana.

Lura da cewa ‘yan takara 20 ne ke neman kujerar shugaban kasar, masu fashin baki sun yi ammanar cewa zai yi wuya a samu wanda zai lashe kashi 50 cikin 100 na yawan kuri’un, wanda hakan zai tilasata zuwa zagaye na biyu.

Daga cikin ‘yan takarar da ke neman maye gurbin shugaba Sirleaf, akwai mataimakinta, Joseph Bokai, da fitaccen dan wasan kwallon kafar nan George Weah, da shugaban ‘yan adawa Charles Brumskine da kuma tsohon jami’in kamfanin Coca Cola, Alexander Cummings, yayin da mace daya tilo ke neman kujerar shugaban kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG