Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Aka Yi Gasar Mawaka A Kano

Kamfanin Meko tare da hadin gwuiwar gidan Rediyon Freedom suka shirya gasar mawaka a Kano wanda ya tattaro mawaka da dama domin baje kolinsu

A wurin gasar shugaban hukumar dake tace fina finai ta jihar Kano, Ismaila Na'abba Afakalla, ya umurci masu shirya gasar da su dinga gauraya fitattun mawaka da masu fina finai da wadanda ke tasowa domin a zakulo masu basira da fasaha ainun.

Nura Bello wanda ya jagoranci gasar ya ce wannan ne karon farko da aka tallata kananan mawaka tare da jan hankalin masu sha'awar shiga harkar nishadi.

A gasar Kabiru Na Mai Rabo ne ya zo na daya a bangaren nanaye kana Abba Fido ya zo na biyu. A bangaren gambara kuma Hanny Billy O shi ne ya zo na daya

Domin Kari

XS
SM
MD
LG