Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Myanmar Ta Gurfanar Da 'yan Jarida A Gaban Kotu


'Yan jarida na zanga zangar kamen da aka yiwa 'yan uwansu
'Yan jarida na zanga zangar kamen da aka yiwa 'yan uwansu

Ana tuhumar wasu ‘yan jaridar kamfanin dillancin labaran Reuters su biyu da aka kama a Myanmar da saba dokar hana fallasa sirrin kasar.

A yau laraba masu gabatar da kara suka bayyana irin caji da ake yi ma Wa Lone, da Kyaw Soe Oo, a wata gajeruwar zaman kotu da aka yi a Yangon. Ranar 12 ga watan Disamba ne aka kama ‘yan jaridar biyu bayan da aka zarge su da samun wasu bayanan sirri da wasu ‘yan sanda biyu suka bas u lokacin da suke cin abinci.

Lauyan ‘yan jaridar ya ce alkalin kotun ya ki ya amince da bukatar bada belin ‘yan jaridar, amma yayi alkawarin cewa zai yanke shawara a zaman kotu na gaba, wanda za a yi ranar 23 ga watan nan na Janairu.

‘Yan jaridar sun hadu da iyalan su, haduwa mai cike da ban tausayi bayan zaman kotun kafin a maida su gidan yari.

A wajen kotun kuwa, ‘yan jarida da yawa sanye da bakaken tufafi ne suka yi gangamin nuna goyon bayan su ga Wa Lone da Kyaw Soe Oo, wasun su na dauke da allunan rubutu dake cewa “aikin jarida ba laifi bane”.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG