Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Ghana Tayi Bikin Ranar Malamai ta Duniya


Mataimakin Shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia

Kamar sauran kasashen duniya jiya Ghana tayi bikin ranar malamai tare da bada kyautuka ga wadanda suka cancanta kamar matar da tayi fice cikin aikin malunta da ta samu kyautar gida

Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tsayar da ranara 5 ga kowane watan Oktoba a matsayin “Ranar Karrama Malaman Makaranta ta Duniya”,ita ma kasar Ghana ta kaddamar da bikin tare da karrama malamai da makarantun da suka yi fice.

Bikin wannan shekarar shi ne karo na 23 da ake girmama malaman da suka fi kowa iya aikin koyarwa da kyaututtukka. Haka ita ma makarantar da tafi kowacce inganci wajen koyarwa da tsarinta tana samun kyauta.

Bana wata mace ce ta lashe kyautar malamar da tafi kowa fice a aikin. Za’a ginawa malamar gida irin na zamani mai dakuna uku a koina take so a cikin fadin kasar.

Sai dai kuma malaman sun roki gwamnati ta taimaka da kayan aiki isassu saboda yawan yaran dake karatu tare da sake masu tsoffin kayan aiki.

Ga Rilwanu Abbas da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG