Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Martin Luther King Ya Cika Shekaru 50 Da Mutuwa


-Dr. Martin Luther King, Jr.
-Dr. Martin Luther King, Jr.

Ranar 4 ga watan Afirilun shekarar 1968 wani farar fata mai rajin wariyar launi ya harbe Martin Luther King ,mai rajin kare hakkin bil Adama, har lahira a birnin Memphis

Duk da yake anyi masa kisan gilla, amma ya bar muna kyawawan halayensa na tsare adalci da tabbatar da zaman lafiya, inji Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke magana a jiya laraba, gameda kwarzon yakin kare 'yancin Bil'Adama Rev. Martin Luther King, a zagayowar ranar da aka yi masa kissan gilla shekaru 50 da suka wuce, a'lamarin d a ya auku a birnin Memphis a jhar Tennessee.

Kashe King da akayi a shekarar 1968 wanda ya biyo bayan kisan da aka yi wa shugaban Amurka John F Kennedy a shekarar 1963, da kuma shima gwarzon yakin kare hakkin Bil'Adama Malcox X a shekarar 1965, wadannan sun haifar da zanga-zanga a wasu manyan biranen Amurka, ciki ko harda nan Washington D C, da Baltimore, da New York da Detroit, da Chicago da birnin Kansas.

A jiya laraba a nan Washington D C, masu zanga zanga sun shiga jerin wadanda suka yi maci cikin lumana daga hasumiyar tunawa da shi king har zuwa babban dandalin taro na kasa anan fadar Amurkan.

A birnin Memphis ma anyi gangami domin tunawa da Dr. king tare da masu jawabai, ciki ko harda dan takarar shugaban kasa a jamiyyar Democrat bannie Sanders,wakilai da kungiyar bakar fata 'yan majalisar dokokin ta tarayya,shugabannin addinai, dana kwadago.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG