Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Shugaban Turkiya Ya Karbi Bakuncin Takwarorinsa Daga Iran Da Rasha


Shugaban Turkiya a tsakiya da bakinsa
Shugaban Turkiya a tsakiya da bakinsa

Shugabannin uku dake goyon bayan bangarori daban daban a yakin Syria da ya kwashe shekaru bakwai ana fafatawa sun hadu a birnin Ankara kasar Turkiya da zummar kawo karshen yakin na Syria

A wani yunkurin ganin an kawo karshen yakin da ake yi a Syria, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayip Erdowan ya karbi bakuncin takwarorin sa na kasashen Iran, Hassan Rouhani, da na Rasha Vladimir Puttin, a jiya laraba, a wani taron kasashen ukku zagaye na biyu.

Iran, da Rasha da Turkiyya, wadanda sune manyan masu goyon bayan sassa daban daban na bangarorin dake gaba da juna a rikicin na Syria tsawon shekaru 7 ana fafatawa, da mamaki a ce kawaye ne domin samun zaman lafiya. Sai kara bayyana yake yi, kowanne daga cikin shugabannin yana takwarorinsa a zaman mai tasiri wajen kawo karshen wannan fadan, kuma kowa ya cimma burinsa a yankin.

A karshen taron kolin, shugabannin da suka halarci taron sun yi alkawarin, za su maida 'yan gudun hijira daga Syria, wannan alkawari na da ma'ana ainun ga hukumomi dake birnin Ankara, ganin ta bada mafaka ga kimanin 'yan Syria milyan uku wadanda rikicin ya tilastawa barin muhallansu. A taron da suka yi cikin sirri, rahotanni suka ce shugaba Rouhani na Iran ya matsawa shugaba Erdogan lamba da ya mika bangaren Syrian da ya kame ga gwamnatin kasar ta Syria, abinda da farko Turkiyyan tace ba zai yiwu ba.

Sai dai kuma sun cimma matsaya wajen sukar rawar da Amurka ke takawa a wannan yakin.

Yanzu dai shugabannin sun amince su sake gudanar da wani taron a Tehran babban birnin Iran

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG