Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Wani Mutum Yayi Ikirarin Yana da Hoda Mai Guba a Motarsa a nan Nirnin Washington DC


'Yansanda sun kewaye motar a kori kura da ta mutumin da ya yi ikirarin yana da mai guba da ake kira anthrax

A nan birnin Washington, DC fadar gwamnatin Amurka, wani mutum ya tuko motarsa a kori kura ya yi shelar yana dauke da hoda mai guba a motarsa lamarin da ya sa 'yansanda suka farmasa suka kamashi

Ahalinda ake ciki kuma, rundunar 'Yansanda ta birnin Washington, sun yi ca a babban dandalin taro dake birnin da ake kira National Mall jiya da tsakar ranar, bayan da wani mutum ya shiga da motarsa kan dandalin yayi ikirarin cewa yana da fodar anthrax mai guba cikin motarsa shigen a kori kura.

Shaidun gani da ido suka ce mutumin ya fita motarsa mai farar fenti, yayi magana da wayar salula dinsa. Yana kan yin magana 'yansanda suka kama shi.

Nan da nan aka kaishi wata rumfa inda za'a tantance ko akwai wannan foda a jikinsa, yayinda aka tura na'urar nan mai kwakwalwa da ake kira robot ta binciki motarsa.

'Yansandan sun ci gaba da kasancewa a sansanin, domin su tanatance yanayin da wannan barzanar ka iya haddasawa.

National Mall wurin da mutumin ya kutsa jiya Talata
National Mall wurin da mutumin ya kutsa jiya Talata

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG